Atiku ya ziyarci Babangida

0

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida a jihar Neja ranar Talata.

Kakakin tsohon mataimakin shugaban kasan Paul Ibe ya ce ya ziyarci Ibrahim Babangida ne domin ya mika gaisuwarsa ganin cewa kwanannan ne ya dawo daga asibiti.

Babangida ya dawo daga kasar Switzerland ranar Lahadi bayan makonni 7 da ya yi a kasar ya na ganin likitoci.

Atiku ya koma garin Minna ne musamman domin ziyarar tsohon shugaban kasan saboda baya kasa a lokacin da ya tafi ta’aziyar rasuwan tsohon gwamnan jihar Abdukadir Kure a watan Janairun da ya gabata.

Daga karshe Paul Ibeh ya yi kira ga mutane da kada su yi ma wannan ziyara ta Atiku da wata fassarar da ba haka ba.

Share.

game da Author