Jam’iyyar PDP za ta lashe zaben 2019

0

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce jam’iyyar sa ta PDP ce zata lashe zaben 2019 a Najeriya.

Jonathan ya fadi hakanne a lokacin da Jerry Gana da ‘yan uwansa su ka kai masa sakamakon kwamitin da jam’iyyar ta nada wanda shi ya jagoranta.

Jonathan ya ce don jam’iyyar PDP ta fadi zaben 2015 ba wai ta kare mata bane. Ta na nan ta na kara shiri da gyara duk kurakuran da ta yi a lokacin zaben.

Ya ce jam’iyyar zata dawo da karfinta domin tana da magoya baya a ko Ina a fadin kasar nan.

Jonathan ya gargadi shugabannin jam’iyyar da su tabbatar da anyi adalci a duk lokacin da za’a gudanar da zabukan wakilai da shugabannin gundumomi da mazabu a kasa Najeriya.

Yace dole a bari mutane su zabi abunda suke so ba tare da wani yayi kakagida akan komai ba.

” Idan har muka bari ana komai yadda ya kamata cikin adalci musamman wajen zabukan ‘yan takara, tabbas za muci nasara akan duk abinda muka sa a gaba.”

“Ya kamata ace an amincewa duk wani jigo a jam’iyyar, sanata ko wani mai rike da kujeran mulki da shugabannin kananan hukumomi da na gundumomi su zama masu zabe ‘yan takara. Yin hakan zai hana duk wani yin kakagida wajen zaben dan takara ko kuma ya nada wa mutane wanda ba sa so”

Daga karshe ya godewa kwamitin sannan ya jinjina wa shugabancin Ahmed Makarfi a jam’iyyar musamman a wanna lokaci da take bukatan hakan.

Share.

game da Author