Kungiyar Kwallon Kafa ta Barcelona ta sha kayi a wasan da ta kara da Kungiyar PSG a kasar faransa.
PSG ta lallasa Barcelona da ci 4 ba ko daya.
Tsohon dan wasana Real Madrid Angel Di Mariya ya saka kwallaye biyu a ragar Barcelona daya a farkon rabin lokaci na biyun kuma bayan andawo hutun rabin lokaci.
Drexler da Cavani sun raba kwallo daya daya cikin kwallaye 4 da suka zira a ragar Barcelona.
A wasa ta biyu kuma kungiyar Kwallon kafa ta Benfica ta lallasa Borussia Dortmund da ci daya mai ban haushi.
A wasannin gobe Arsenal Zata Kara da Bayern Munich, sannan Real Madrid za ta goge raini ne da Napoli a filinta dake Madrid.