Uwargidan Shugaban mai barin gado Muhammadu Buhari, ta damƙa takardu da Ofishin Uwargidan Shugaban Ƙasa (First Lady) ga Oluremi Tinubu, matar Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu.
A lokacin da A’isha ke damƙa mata kwafen fayil-fayil na wasu ayyukan da ofishin ya yi a tsawon zaman ta shekaru takwas a Fadar Shugaban Ƙasa, ya bayyana wa matar Tinubu cewa Ofishin Uwargidan Shugaban Ƙasa dai haramtacce ce, domin babu shi a cikin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.
“Shi dai wannan Ofishin Uwargidan Shugaban Ƙasa (First Lady), kamar yadda ki ka sani, babu shi a cikin dokokin Najeriya. To amma mu na amfani da shi ne wajen samun ƙima, ta hanyar gudanar wa jama’a wasu ayyukan agaji da jinƙai da kulawa.”
An yi ƙwarya-ƙwaryar taron, wanda A’isha Buhari ta riƙa kewayawa da Oluremi Tinubu, ta na nuna mata wurare a cikin ofis ɗin, tare kuma da fayyace mata irin ayyukan da su ka rataya a wuyan ‘First Lady’.
Yayin da za a rantsar da Bola Tinubu a ranar 29 Ga Mayu, a ranar ce ita kuma Remi Tinubu za ta zama First Lady kenan.
Har ila yau dai, A’isha ta damƙa wa Remi Tinubu tambarin Ƙungiyar Matan Shugabannin Ƙasashen Afrika, wanda ita ce shugabar su.
Hakan ya na nufin kenan daga ranar Litinin shugabancin ƙungiyar zai koma a hannun Remi Tinubu.
A’isha ta jaddada cewa ta na da yaƙinin Remi Tinubu za ta yi bakin ƙoƙarin ta.
Ta kuma sanar da ita irin wasu ayyukan jinƙai da ofishin ya yi, wanda ta ce ya kamata Remi ta yi nazarin su, a matsayin sanin-makamar-aiki a wurin ta.
Oluremi ta ce duk da dai a baya ya yi tsawon shekaru takwas a matsayin ‘First Lady’ a Jihar Legas, yanzu kuma ta cika shekara 12 a Majalisar Dattawa, aiki da Fadar Shugaban Ƙasa zai zame mata sabon abu.
Daga nan ta jinjina wa A’isha Buhari dangane da irin rawar da ta taka a shekaru takwas da ta yi kan kujerar.
Discussion about this post