Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta bayyana cewa ta saurari kararrakin fyade 35 a cikin watanni hudu a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Usman Gomna, ya sanar da haka wa manema labarai ranar Laraba a garin Dutse.
Gonna ya ce rundunar ta saurari kararrakin fyade fiye da sauran laifuffuka kamar su garkuwa da mutane da kai wa mutane hari.
” A cikin watanni hudu da suka gabata jihar ta samu raguwar wadanda aka yi garkuwa da su zuwa mutum 10 a cikin watanni hudu.
Gomna ya yi kira ga iyaye da su rika sanya wa ‘ya’yansu ido da kula da zirga-zirgan su, musamman yara kanana da ake dora musu talla suna gararamba a tituna suna talla.
” A Mafi yawan lokutta an fi yi wa yara kanana saboda gararamba da suke yi ba tare da kulan Iyayen su ba.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya gwamnatin jihar ta kafa dokar yanke wa masu fyade a jihar hukuncin kisa.
Dokar ya kuma ce za a biya wadanda aka yi wa fyaden naira 500,000.
Discussion about this post