TABARBAREWAR TSARO: A yi wa ‘yan bindiga luguden juju, surkulle da tsatsube-tsatsube a ga aiki da cikawa -Inji wani basarake

0

Tsohon Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Ekiti, Gbadebo Adedeji, ya yi kiran a yi amfani da siddabarun gargajiya na tsatsube-tsatsuben iyaye da kakanni da aka san Afrika da su, domin a yaki matsalar tsaro, musamman ‘yan bindiga masu kashe mutane da yin garkuwa da su.

Adedeji wanda shi ne Owa Ooye na Okemesi-Ekiti ya bayyana cewa an yi sakaci da aka yi amfani da tsatsube-tsatsuben gargajiya da tuni an kakkabe ‘yan ta’adda.

“In banda sakaci ya za a yi a ce wai an sace basarake guda. Ya za a sace Oba sukutum sai ka ce an saci dantsako. Watsi da lakanin magungunan gargajiya ya sa haka ke faruwa.

“Rungumar addini da Afrika ta yi ya sa har aka yi watsi da surkullen da aka gada iyaye da kakanni. A zamanin da can ai da surkullen juju ake tafiya yaki kuma a yi amfani da shi a yi galaba kan abokan gaba.

“A wasu kasashe al’adu hanya ce ta samar wa kasa makudan kudaden shiga. Amma mu nan abin ba haka ya ke ba. Mun saki al’adun mu yanzu kuma abin ya dame mu.”

Da ya ke wa manema labarai jawabi wajen bayyana ranar rufe gagarimin bikin al’ada na Okemesi, wanda za a rufe kasaitaccen bikin a ranar 8 Ga Mayu, ya kara da a gaggauta kawar da kashe-kashe da hare-haren ‘yan bindiga ta hanyar yi masu lugjden ‘agumu“, sagau, surkulle, tsatsube-tsatsube da amfani da duk wani lakanin gargajiyar da aka san zai kawar da su da gaggawa.

Share.

game da Author