Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa a ranar Juma’a ya amince da karin kashi 50 cikin 100 na kudin ciyar da abinci ga dalibai a makarantun kwana na jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan ilimi Yusuf Chamo ya fitar a Dutse babban birnin jihar.
Kwamishinan ya ce an yi karin ne domin tabbatar da an samar da abinci mai inganci da gina jiki ga dalibai a fadin jihar.
“Karin ya zama dole dubi da hauhawar farashin kayayyaki da ake fama da shi a ƙasar.
“ Sannan kuma Gwamnatin jihar ta samu korafe-korafe daga ‘yan kwangilar da ke aikin samar da abinci ga dalibai a makarantun.
“Saboda haka, an kafa wani kwamiti da zai duba yanayin da kuma samar da mafita cikin gaggawa,” in ji kwamishinan.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta yanke wannan shawara ne domin a ceto lamarin da kuma tabbatar da tsafta ga irin abincin da ake baiwa dalibai.
Discussion about this post