Rundunar ‘yan sanda a Legas ta kama batagari 590 a wurare daban-daban a fadin jihar daga ranar 13 ga watan Fabrairu zuwa 13 ga Maris.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Legas ranar Laraba.
Hundeyin ya ce an kama wadanda ake zargin ne a yayin samamen da da ‘yan sanda suka kai musu.
Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Adegoke Fayoade ne ya bayar da umarnin kai samamen, biyo bayan korafe-korafe da mazauna yankin suka yi.
A karshe dai za a maka su duka kotu domin fuskantar hukunci.
Discussion about this post