Gwamnatin jihar Taraba ta tabbatar da bullar zazzabin Lassa a jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar Gbangsheya Buma a sanar da haka ranar Talata yana mai cewa daga cikin mutum 9 da aka yi wa gwaji mutum 8 sun kamu da cutar, kuma suna kwance a asibitin gwamnatin tarayya dake Jalingo.
“Mun aika da samfurin jinin mutum 9 da muke zaton sun kamu da cutar wurin gwajin dake Abuja. Sakamakon da ya dawo ya nuna mutum 8 sun kamu.
Buma ya ce hukumar NCDC za ta hada hannu da asibitin FMC Jalingo da sauran jami’an lafiyan dake jihar domin dakile yaduwar cutar.
Bayan haka shugaban asibitin FMC Jalingo Joseph Kuni ya ce daga watan Janairu zuwa Fabrairu 2024 mutum 19 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar.
Ya kuma ce a tsakanin wannan lokacin sun aika da sanfurin jinin mutum 105 da ake zargin sun kamu da cutar inda sakamakon da ya dawo ya muna cewa mutum 60 sun kamu, mutum 36 basu dauke da cutar.
“Yanzu mutum 10 ne ke killace a fannin kula da masu fama da cutar na asibitin mu.
Kuni ya ce har yanzu basu da wurin gwajin cututtuka a asibitin a dalilin gobarar da aka yi a shekarar bara da hakan ya sa suke aikawa da samfurin jini zuwa wuraren gwajin dake Abuja ko jihar Bauchi.
“Bana jami’in lafiya daya ya kamu da cutar kuma ma ya warke har an sallame shi.
Abubuwan da za a kiyaye don gujewa kamuwa da zazzabin lassa
Tsaftace muhalli: A Rika tsaftace muhalli a ko da yaushe. A kau da datti a kowani lokaci sannan a rika goggoge wurare.
Zubar da shara: Idan aka Tara shara kada a rika zubar da shi kusa da gida a rika kaiwa can waje.
Killace Abinci da ruwan Sha: Yin haka zai taimaka wajen hana bere ko kwari shiga cikin abinci ko ruwan sha.
Dafa nama: Kafin a dafa nama kamata ya yi a rika wanke shi da ruwan gishiri domin kashe duk wasu kwayoyin cuta dake jikin naman. A tabbatar naman ya dahu sosai kafin a ci.
Tsafta: A yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu kafin da bayan an ci a inci sannan idan an kammala amfani da ban daki.
Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbatar sun nemi magani da zarar allurar da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cuter ya sole su.
Kona daji: Kona daji na daga cikin hanyoyin dake Koro beraye zuwa cikin gidajen mutane. A rika kiyayewa wajen kona dazukan dake kewaye da mu. Mai makon haka a rika feshin magani.
Wanke gawa a cikin daki: Shima hakan na da illa matuka. Maimakon a rika wanke a rika wanke gawa a cikin gida a rika yin sa a waje ko Kuma a inda ya kamata.
Discussion about this post