Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta bayyana cewa an samu ragowar yawan mace-macen ƙananan yara sabbin haihuwa zuwa ‘yan shekaru 5 a cikin 2022.
WHO ta ce a cikin 2022, ƙananan yara miliyan 4.9 ne suka mutu sanadiyyar cututtukan da za a iya magance su cikin gaggawa a faɗin duniya.
Ƙiyasin da ya fito daga Cibiyar Ƙididdigar Matattun Ƙananan Yara ta Hukumar Lafiya ta Duniya (UN IGME), ya nuna cewa an samu ƙarancin yawaitar mutuwar ƙananan yara sosai a duniya, idan aka kwatanta da shekaru 30 ko 24 baya da suka gabata.
Rahoton da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya buga, ya nuna cewa mace-macen ƙananan yara sun tafi da kashi 60 bisa 100, daga yara 93 duk cikin kowane yara 1,000 da aka haifa a shekarar 1990, zuwa yara 37 a duk cikin yara 1,000 da aka haifa a shekarar 2022.
Rahoton na Hukumar Lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WHO) ya nuna cewa a yanzu ƙananan yara ha su saurin mutuwa kafin su kai shekaru biyar da kashi 51 cikin 100, tun daga shekarar 2000 zuwa yau.
Rahoton ya tattaro bayanan cewa ƙananan ƙasashe marasa ƙarfin tattalin su ma sun samu wannan ci gaba, musamman ta hanyar maida hankali wajen kula da lafiya a matakin farko, abin da ya haɗa da ƙara inganta kiwon lafiyar ƙananan yara.
“Misali, a ƙasashe irin su Cambodia, Malawi da Mongoliya da Ruwanda, an samu ragowar mace-macen ƙananan yara ‘yan ƙasa da shekaru 5 zuwa kashi 75 bisa 100 tun daga 2000 har zuwa yau.
“To amma kuma binciken ya nuna cewa duk da irin wannan gagarimin ci gaba da aka samu, har yanzu akwai sauran jan aiki a gaba domin kakkaɓe cututtukan da ke kashe ƙananan yara da matasa, kuma cututtukan duk za a iya kawar da kafin su yi kisa.
“Daga cikin yara ƙanana miliyan 4.9 da suka mutu a duniya ta hanyar cututtuka daban-daban, to kusan rabin su duk yara ne sabbin haihuwa.
“Sai dai kuma rahoton ya ci gaba da cewa wasu miliyan 2.1 na ƙananan yara da matasa ‘yan shekaru 5 zuwa 24 sun mutu a duniya.
“Amma yawancin mace-macen sun fi faruwa ne a ƙasashen Afrika da kuma Kudancin Asiya.”
Haka nan kuma rahoton ya ƙara da cewa yawanci musabbabin mutuwar ya kama daga dalilai na haihuwar bakwaini, amai da gudawa, zazzaɓin maleriya da tangarɗa yayin haihuwa da kan galabaitar da jinjiri da kuma cutar sanyin limoniya.
Discussion about this post