Majalisar Dattawa ta yi wa Sanata Abdul Ningi yankan-kunkurun-Bala, inda ta dakatar da shi tsawon watanni uku, sakamakon zargin da ya yi cewa an yi wa Kasafin 2024 cushen Naira Tiriliyan 3.
Ningi, Sanatan Bauchi ta Tsakiya, kuma ɗan PDP, an dakatar da shi ne a ranar Talata.
Sai dai kuma shugabannin majalisar sun amince cewa idan Ningi ya rubuta takardar neman afuwa, to za a canja tunanin yi masa afuwa ko kuma a ci gaba da dakatarwar.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya bayyana sanarwar dakatar da Ningi, bayan dakatarwar ta samu goyon bayan mafiya yawan mambobin Majalisar Dattawa ɗin, a zaman da Majalisar ta yi matsayin kwamitin su baki ɗaya.
“Ina sanar da dakatar da Ningi tsawon watanni uku daga duk wasu aikace-aikace da suka shafi Majalisar Dattawan Najeriya,” inji Akpabio.
Dakatarwar dai ta biyo bayan ƙorafin da Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Kuɗaɗe, Sanata Adeola Olamilekan.
Ningi wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar Sanatocin Arewa (NSF), kwanan nan ne ya shaida wa BBC Hausa cewa ‘yan majalisa sun kira mai bin diddigin kuɗaɗe mai zaman kan sa, wanda ya bankaɗo yadda aka yi cushen Naira Tiriliyan 3 cikin Kasafin 2024.
“Misali, muna da kasafi na Naira tiriliyan 28, amma bayan an yi bincike da bin diddigi, an gano cewa tantagaryar kasafin kuɗin Naira tiriliyan 25, sauran tiriliyan 3 kuma cushe ne aka yi. To me za a yi da Naira tirliyan ukun da aka cusa a kai?”
Idan ba a manta ba, su ma sanatocin Arewa sun tunkari Akpabio, inda suka zarge shi da cusa Naira tiriliyan 4 a cikin kasafin 2024.
Idan za a tuna, a ranar Litinin Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata zargin da Sanata Ningi ya yi, inda ta kira shi tantirin maƙaryaci.
Discussion about this post