Ƴansanda a Jihar Abiya sun tabbatar da fasa wani gidan da aka killace mata su na haihuwar jirajiran da ake sayarwa, wanda a Turance ake kira ‘baby factory’, a garin Aba.
Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Abiya, Maureen Chinaka, ta bayyana wa manema labarai wannan wawan kamu da jami’an tsaro su ka yi, a ranar Juma’a.
A zantawar da ta yi a su a Umuahia, babban birnin Jihar Abiya, Maureen ta ce an ceto ƙananan ‘yan mata masu ciki su 16 a gidan, waɗanda shekarun su suka kama daga 17 zuwa 26.
Ta ce 13 daga cikin ‘yan matan ‘yan asalin Jihar Akwa Ibom ne, biyu kuma daga Kuros Riba, sai ɗaya kuma ‘yar asalin jihar Ebonyi ce. Dukkan jihohin dai a kudancin Najeriya suke.
Maureen wadda Mataimakiyar Sufurtandan ‘Yan Sanda ce, ta ce ‘yan sanda sun yi wa gidan dirar-mikiya a ranar Alhamis da dare.
Ta ƙara da cewa a gidan har ila yau an ceto ƙananan yara takwas, waɗanda biyar daga cikin su maza ne, sai kuma uku mata.
Yaran sun kama daga shekaru biyu zuwa shekaru 11.
Ta ce an kuma kama mutum biyu da ake zargi, mace ɗaya, namiji ma ɗaya. Su ne ake zargin sun ɓoye matan a cikin gidan, waɗanda ake ɗirka wa cikunna su na haihuwa.
Waɗanda ake zargin dai akwai wata mace mai shekaru 29, wai ita Onyinyechi Okoro, sai kuma namiji mai suna Ekene Okezie, mai shekaru 32.
Discussion about this post