Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane a kan hanyar Buruku zuwa Kaduna a ranar Alhamis.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Mansir Hassan, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Kaduna, inda ya ce ‘yan bindigar sun arce bayan ƴan sanda sun yi musu luguen wuta babu ƙaƙƙautawa a lokacin da suke kokarin sace mutanen.
A ranar 21 ga Maris, da karfe 1300 na safe, jami’an 47PMF da ke aiki a Buruku sun yi nasarar dakile wani yunkurin yin garkuwa da wasu mutane a kan hanyar Buruku zuwa Kaduna.
Musayar wuta da aka yi ya tilasta wa ‘yan bindigar arcewa cikin daji. Sai dai duk da haka ‘yan bindigar sun samu munanan raunuka yayin arangamar,”
Hassan ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Audu Ali, ya yabawa jarumtaka da gaggawar matakin da ‘yan sandan suka dauka na hana abin da ka iya zama mummuna lamari. Ya kuma bukaci jama’a da su sanya ido tare da kai rahoto ga hukuma cikin gaggawa duk wans basu amince da zirga-zirgar sa ba a wannan yanki.
Discussion about this post