Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta buga sanarwar cigiya da farautar fitaccen malami Idris Abdul’aziz, wanda aka fi sani da Dutsen Tanshi.
Ya gudu daga jihar bayan ya yi iƙirari da zargin cewa Gwamna Bala Mohammed ya taso shi a gaba ya na musguna masa.
Gwamnatin Jihar Bauchi na zargin da cajin sa da “tunzira jama’a yin bore, yin ɓatunci da ɗirka saɓo a musulunce.” Sai dai kuma duk ya ƙaryata zargin da ake yi masa.
A ranar Alhamis Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta buga sanarwar cigiya da farautar sa, makonni biyu bayan ya arce daga jihar.
Sanarwar dai har ta na ɗauke da hoton sa, inda ake cajin sa da laifin saɓa umarnin kotu da ƙin yi wa kotu biyayya.
A cikin sanarwar cigiyar, an ambaci cewa za a bada lada ga dukkan wanda ya san inda malamin ya ɓoye, kuma ya bada bayanin da aka je aka kamo shi.
Sai kuma lauyan sa ya shaida wa wakilin mu cewa buga sanarwar cigiyar ba sabon abu ba ne. Ya ce kawai dai gwamnatin jiha na kashe kuɗaɗen jama’a don su rufe bakin masu adawa.
Gudun Hijirar Dutsen Tanshi:
Sheikh Dutsen Tanshi ya yi gudun hijira, ya na zargin Gwamna Bala na neman yi masa ƙarfa-ƙarfa.
Fitaccen malamin addinin Musulunci da ke Bauchi, Sheikh Idris Abdul’aziz, wanda aka fi sani da Dutsen Tanshi, ya arce daga garin Bauchi yayin da ake tsakiyar dambarwar shari’ar sa da kuma takun-saƙar da ke tsakanin sa da Gwamna Bala Muhammad na Bauchi.
Sheikh Idris ya shiga fagen siyasa tsamo-tsamo a kamfen ɗin 2023, inda ya riƙa kiran kada a sake zaɓen Gwamna Bala, wanda ake wa laƙabi da Ƙauran Bauchi.
Idris ya nuna ƙarara ya na goyon bayan ɗan takarar APC, Abubakar Sadiq, wanda ya faɗi zaɓen a yawan ƙuri’u da kuma Kotun Ƙoli.
Lauyan sa Ahmad Musa ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa makamin ya tsere gudun-hijira, bayan da jami’an tsaro suka yi wa gidan sa da ke unguwar Dutsen Tanshi dirar-mikiya da niyyar kama shi a ranar 24 ga Janairu, bisa umarnin kama shi daga sammacin kotu.
“Abdul’aziz ya fice daga Bauchi ya yi gudun-hijira, saboda matsin-lambar da ya ke fuskanta, wato ƙoƙarin sake kama shi da gwamnatin Jihar Bauchi ke shirin yi.
“An shirya masa caje-cajen zargin yin kalaman ɓatanci a Musulunci. Ya samu nasarar ficewa daga Bauchi zuwa inda zai zauna ba tare da tsangwama ba.” Cewar lauyan.
“Duk da cewa akwai shari’ar sa da ake yi a Kotun Ɗaukaka Ƙara da ya shigar a ranar 24 ga Janairu, 2024, sai kuma Alƙalin Babbar Kotun Musulunci ta Bauchi, Hussaini Tiraki ya bai wa ‘yan sanda warantin kama malamin.
“An tura ‘yan sanda sama da 250 da ‘yan sibil defen domin kamo shi. Sun kewaye gidan sa ranar Alhamis, 25 ga Janairu, amma ba su same shi ba. Kuma ba su samu wani abu da ke nuna ya na da wani laifi ba.” Inji lauyan sa Musa.
Bayanai sun nuna cewa an tura cincirindon ‘yan sanda ne gidan malamin bayan da wani ɗalibin sa ya shiga Tiktok ya yi rantsuwar cewa ba za su bari a tafi da malamin su ba, sai dai a ranar a yi mutuwar-kasko.
Baya ga rigingimun siyasa da ke kan malamin, ya shiga tsomomuwa yayin da ya ce ba ya neman taimakon kowa, har ga Annabi SAW, sai ga Allah kaɗai.
A kan haka ne mabiya aƙidar Salafiyyah da Izala yawancin su, suka goyi bayan sa, yayin da mabiya ɗariƙu suka riƙa neman a kama shi a hukunta shi.
Bayan ƙarar da aka maka shi, malamai sun shiga tsakani har aka sake shi a wancan lokacin.
Discussion about this post