Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa cinkoson ma’aikata ya yi yawa sosai a Hedikwatar CBN da ke Abuja.
Ya ce wannan cinkoson da ma’aikata suka yi ɗaya daga cikin dalilan da suka sa za a kwashe wasu ma’aikatan wani ɓangare na bankin daga Ábuja a maida su Legas.
Cardoso ya bayyana haka a lokacin wata tattaunawa da gidan talabijin na Arise TV, ranar Litinin.
Da ya ke magana dangane da ce-ce-ku-ce kan batun maida wasu ma’aikatan zuwa Legas, Cardoso ya ce wasu sun yi ƙoƙarin maida lamarin siyasa ko kuma abin yi wa furucin kisisina da kwatagwangwamar siyasa.
Ya ce bai kamata a sa don rai ko siyasar ɓangaranci a muhimmin wuri kamar CBN ba.
“Lallai Hedikwatar CBN da ke Abuja cunkushe ta ke da ɗimbin ma’aikata. Dalili kenan na ya sa idan aka kwashe wani ɓangaren ma’aikatan zuwa Legas, za a iya magance matsalar cinkoson.”
Ya ce shi CBN banki ne na ƙasa, kuma kowace jiha akwai reshen sa.
Sai dai kuma ya ce a lamarin da za a jibge wasu ƙwararru a wuri ɗaya, amma kusan ko’ina ana buƙatar su, abu ne da zai iya daƙile ƙoƙarin bankin.
Ya ce bankunan kasuwanci na ƙasar nan kusan duk a Legas Hedikwatar su ta ke. Don haka ba dabara ko fa’ida ba ce sashen kula da bankunan da ke CBN ya ci gaba da kasancewa a Abuja, domin ayyukan sashen duk a Legas ya ke.
Discussion about this post