Kungiyar likitocin MSF ta bayyana cewa akalla yara 3,965 suka karbi maganin cutar bakin dauro a asibitocin ta dake jihar Borno daga watannin Oktoba zuwa Disemba 2023.
Kungiyar ta kuma ce a cikin watanni 12 da suka gabata yara 9,618 ne suka karbi maganin cutar a asibitocin kungiyar da suka hada da asibitin yara na Gwange, Nilefa Kiji da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko dake jihar da kungiyar ke aiki da su.
MSF ta tabbatar cewa an samu karin yara da suka kamu da cutar a shekarar 2023 fiye da yawan da aka samu a shekarar 2022.
Jami’in yada labarai na MSF Abdulkareem Yakubu ya ce ya zama dole gwamnati ta zage damtse wajen yi wa yara kanana allurar rigakafin cutar a jihar.
Wani likita dake aiki da MSF Abdulwahab Mohamed rashin tsaro na daga cikin matsalolin dake hana a samu kashi 95% na yi wa yara kanana allurar rigakafin cutar a jihar.
Manajan asibitin Gwange Jombo Tochukwu-Okoli ya ce bullowar cututtuka kamar su Korona, Diphtheria, Zazzabin cizon sauro da dai sauran sun na daga cikin matsalolin da suka hana yin wa yara rigakain cutar.
Bakon Dauro
Bakon dauro cuta ce da kwayoyin cutar ‘Virus’ ke haddasa ta sannan rashin daukan mataki kan cutar ne na yin ajalin yara kanana.
Akan kamu da bakon dauro ta hanyar shakar kwayoyin wannan cuta ta iska, yin tari, yawan zama da mai dauke da cutar,sannan cutar kan dauki tsawon kwanaki 14 kafin ya nuna alamu.
Alamun bakon dauro sun hada da zazzabi,tari,mura, kurarraji, rashin iya cin abinci da sauran su.
Malaman asibiti sun yi kira ga mutane da su hanzarta zuwa asibiti idan aka ji ba daɗi a jiki.
Yi wa yara allurar rigakafi a lokacin da ya kamata na daga cikin hanyoyin samun kariya daga kamuwa da cutar bakon dauro da sauran su.
Discussion about this post