Hukumar Dakile Yaduwar Cutar Kanjamau ta Kasa NACA ta yi kira ga masoya su yi taka-tsantsan da kula a lokacin da ake shagulgulan ranar masoya musamman a wajen yin Jima’i
Shugaban hukumar Gamboru Aliyu ya yi wannan kira ne ranar Lahadi wanda jami’in hulda da jama’a na hukumar Toyin Aderibigbe ya sanar wa manema labarai.
Bisa ga sakon Aliyu ya gargadi masoya da su rika tattauna yadda za su kare kansu daga kamuwa da cututtuka yayin da suke jima’I sannan su dage wajen yin gwajin cutar Ƙanjamau a tsakanin su.
Ya ce yin haka na daga cikin hanyoyin wayar da kan mutane da dakile yaduwar cututtuka a tsakanin masoya musamman a wannan rana ta masoya.
Aliyu ya ce a ranar masoya ta duniya da ake yi ranar 14 ga Fabrairu ta kowace shekarar hukumar za ta gudanar da taro domin wayar da kan mutane kan cututtukan da ake kamuwa da su ta jima’I da hanyoyin samun kariya daga kamuwa da su.
Discussion about this post