Kotun majistare dake Surulere a jihar Legas ta bada belin wata tsohuwa mai shekara 62 Yemis Olukemi akan naira 30,000 bayan ta ture wani ma’aikacin Kamfanin wutar lantarki na EKEDC yayin da yake kokarin cire mata wuta.
Alkalin kotun Olubunmi Gbenga ta kuma ce Yemis za ta gabatar da shaida daya domin cika sharaddan belin da kotu ta bada.
Okubunmi ta ce za a ci gaba da shari’a ranar 20 ga Fabrairu.
Rundunar ‘yan sandan jihar sun gurfanar da Yemis a kotun bisa laifukan da suka hada da tada hankalin mutane, hada wuta ba bisa ka’ida ba da neman yin kisa.
Dan sandan da ya shigar da karar Christopher Okoliko ya ce Yemis ta aikata wadannan laifukan ranar 17 ga Janairu a gidanta dake lamba 46, layin Bolaji Banwo a Aguda Surulere.
Okoliko ya ce Yemis ta tunkude ma’aikacin Kamfanin wutan lantarkin mai suna Abolore Muritala yayin da yake kokarin cire mata wuta da ta hada ba bisa ka’ida ba.
Bayan ya faɗo tim kasa, sai Yemis ta sake haɗa wutan kuma.
Discussion about this post