Sojojin Najeriya dake aiki a karkashin rundunar ‘Operation Safe Haven OPSH’
sun bankaɗo masana’antar hada bindigogi a kauyen Pakachi dake karamar hukumar Mangu a jihar Filato.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar James Iya ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a garin Jos.
Iya ya ce dakarun sun kama makamai daban-daban sannan sun kama wani mutum daya a wannan kamfani.
“A kokarin da muke yi na tabbatar da zaman lafiya a jihar Filato dakarun mu sun banƙado masana’antar kera bindigogi dake tsaunikan kauyen Pakachi a karamar hukumar Mangu.
“A kamfanin sojoji sun kama mutum daya da makamai da dama a wurin.
“Mai kamfanin Nuhu Meshach ya gudu saidai sojoji sun fara farautar sa.
Ya ce mutumin da malaman da suka kama na tsare a hannun rundunar OPSH domin ci gaba da gudanar da bincike.
Iya ya ce kamen da suka yi na daga cikin nasarorin da dakarun suka samu wajen samar da zaman lafiya a jihar Filato.
Discussion about this post