Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta dauki matakai domin kawar da matsalar ficewar jami’an lafiya zuwa kasashen waje.
Ministan lafiya Muhammad Pate ya sanar da haka a Abuja ranar Laraba.
Pate ya ce gwamnati ta dauki ma’aikatan lafiya sama da 2,000 a cikin watanni shida domin rage ficewar ma’aikatan lafiya daga kasar nan zuwa kasashen waje.
Ya ce gwamnati ta karo kwararrun Ungo zoma domin inganta lafiyar mata a asibitocin 1,400.
“A cikin watanni shida da suka gabata gwamnati ta karo jami’an lafiya da suka hada da likitoci, ma’aikatan jinya, ungo zoma da CHEW da hakan ya sa aka samu karin mata 230,000 dake haihuwa a asibiti.
Ficewar jami’an lafiya daga Najeriya zuwa kasashen waje matsalace da ta dade tana cutar da fannin kiwon lafiyar kasar nan da gwamnati ba iya kawo karshen sa ba a tsawon lokaci da ake ciki.
Bincike ya nuna cewa likitoci sama da 5,000 ne suka fice zuwa kasar UK daga 2015 zuwa 2022.
Kungiyar Likitocin Najeriya NMA ta yi kira ga gwamnati da ta samar da ababen more rayuwa musamman inganta fannin kiwon lafiya da samar da tsaro domin samar da ci gaba a kasar.
Rashin kayan aiki, rashin ingantaccen wurin aiki, rashin biyan ma’aikata albashi mai tsoka da dai sauran su na daga cikin dalilan da ya sa jami’an lafiya ke ficewa daga kasar nan.
Pate ya ce gwamnati ta dauki matakai domin inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a kasar nan.
Discussion about this post