Yayin da ake fama da hauhawar farashin kaya musamman na abinci a kasuwanni manoman tumatir, tattasai da albasa a kananan hukumomin Garun Mallam da Kura sun fara siyar da amfanin gonakinsu a kasuwanni.
Zuwa yanzu babban kwandon tumatir ana samunsa kan naira 30,000 daga naira 4,000 din da aka siyar a wannan lokaci a shekarar bara.
Manoma sun koka kan wasu matsaloli da dake ci musu tuwo a kwarya a noman ranin da suke yi wanda suka hada da yawan canjin a farashin kaya, tsadar farashin kayan aikin noma, rashin samun tallafi daga gwamnati, rashin ingantaccen wurin ajiyan amfanin gona da sauran su.
Matsalolin da manoma ke fama da su
Matsalolin da suka hada da tsadar taki, maganin feshi, rashin ingantaccen wurin ajiyan amfanin gonna, rashin samun tallafi daga gwamnati da kuma rashi na’urorin sarrafa kayan gona.
Sani Danladi Shugaban kungiyar manoman tumatir NATPAN ya ce rashin ingantaccen wuraren ajiyar amfanin gona da rashin na’urorin sarrafa amfanin gona na daga cikin matsalolin da suke fama da su.
“Yanzu manoman tumatir za su sami kudi saboda farashin da ake siyar da tumatir ya yi tsada amma idan har sauran manoman suka fara zuwa da nasu amfanin gonan farashin zai karye, manoma za su iya yin hasara
“Muna bukatan tallafin daga gwamnati musamman ta fannin rage farashin taki da maganin feshi zuwa farashi mai sauki sannan da samar da na’urar da zai rika sarrafa tumatir zuwa na gwangwani ko kuma gari domin rage wa manoma asarar da suke yi a lokutta da dama.
Sauran matsalolin da manoman ke fama da su sun hada da cire tallafin man fetur, karyewar darajar naira, rashin tsaro da canjin yanayi.
Zuwa yanzu kasashen kamar Ghana da Kamaru na shigowa kasuwani irin haka suna siyan kaya a farashi mai sauki suna komawa da su kasashen su suna siyarwa da tsada, suna samun riba mai yawa.
Tumatir na dauke da sinadarin inganta lafiyar mutum sannan yana daga cikin mahimman kayan hadin da ake bukatan wajen girka abinci ko miya kowace iri.
Discussion about this post