Kociyan Super Eagles, Jose Peseiro ya bayyana cewa Zaidu Sanusi na buga masa irin kwallon da ta ke so kuma ya gode masa matuka.
Da yake hira da manema labarai bayan wasan Najeriya da Angola Peseiro ya ce ƴan wasan Super Eagles gaba ɗayan su na buga masa abinda ya hore su da su buga a filin wasa.
Najeriya ta lallasa Angola da ci ɗaya mai ban haushi a wasan Kwata final da aka buga a Abidjan ranar Juma’a.
An tambayi Kociya Peseiro game da wasu kurakurai da Zaidu ya yi a lokacin wasa inda ya ba da amsar cewa ” Salon wasan da Najeriya ta buga yana da wuyan gaske musamman ga wurin da Zaidu ke bugawa.
” Zai taso daga baya ya cilla gaba sannan ya sake juyowa da gudu ya dawo tsare gida duk a lokaci guda ba tare da ya tsaya ba.
” Eh, akan samu kuskure a wasu lokuttan, kowa yana samun irin wannan kuskuren. Amma a wasan yau kam an samu ci gaba matuka. Ƴan wasan Super Eagles dukkan su sun yi abinda ya kamata kuma sun yi kokarin gaske matuka.
Discussion about this post