Ministan Abuja Nyesome Wike a ranar Litini ya bayyana cewa rashin isassun kayan aiki da motocin sintiri na daga cikin matsalolin dake hana yakan ta’addanci da ake fama da a Babban Birnin Tarayya.
Wike ya fadi haka ne yayin da yake ganawa da manema labarai inda yake karin haske kan dalilan da ya sa ake samun karuwa a ta’addanci da yin garkuwa da mutane a Abuja.
Wike ya tabbatar wa mutane cewa nan ba da dadewa ba Shugaban kasa Bola Tinubu zai ware wasu makudan kudi domin kawo karshen matsalolin.
Ya ce za a yi amfani da wadannan kudade domin samar da kayan da za a bukata domin yakan mahara.
“Abin mamaki ne a ce daidai da na’urar bin sawun ‘yan bindiga domin gano maboyar su na zamani jami’an tsaron mu basu da su.
Ya ce jami’an tsaro na bukatan kayan aiki irin na zamani wadanda za su taimaka wajen yakan ta’addanci a Abuja.
Discussion about this post