Wata kazar da ta shafe shekaru kusan 22 a duniya ta mutu.
Kazar mai suna Peanut, ita ce kaza mafi daɗewar tsawon shekaru a duniya.
Ta mutu ta na da shekaru 21 da kwanaki 238 da ƙyanƙyashewa.
Kundin Tarihin Duniya ya rattaba kazar a matsayin wadda ta fi kowace kaza dadewa a duniya.
Ta rasu ranar Kirsimeti, a gidan mai kazar da ke Michigan, Amirka.
Mai kazar mai suna Marsi Darwin, ta nuna alhini da jimamin rasuwar Peanut, wadda ta ce “kazar ta zame masu kamar wata ɗaya daga cikin iyalin su ta jini.”
Discussion about this post