Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja ta ce dukkan mazauna birnin su kwantar da hankulan su, domin ƙarar fashewar wani abu da aka yi tunanin bam ne, ba bam ba ne.
Ƙarar wadda ta tashi a unguwar Maitama, ta tashi hankalin mazauna yankin a ranar Laraba.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan FCT Abuja, Josephine Adeh, ta ce wata kwantinar jibge shara ce ta sha zafin rana, ta yi bindiga a Maitama.
Rahotonni dai a ranar sun nuna yiwuwar fashewar bam ce, lamarin da ya jefa mutane da dama cikin tsoro, firgici da zaman ɗar-ɗar.
‘Yan Sanda sun ce fashewar ƙarar ta rufu ne a wani wurin tara bola a wata kwantinar ƙarfe, a Maitama, wajen Ofishin Hukumar BPE.
Sun ce wasu masu kwasar shara biyu sun ji ciwo, kuma su na asibitin Maitama ana kulawa da su.
Ƙarar dai ta fashe ne ranar Laraba wajen 11:45 na rana.
Lamarin ya faru a lokacin da mazauna Abuja da kewaye ke zaman zullumin fama da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Discussion about this post