Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Oyo, Iyiola Oladokun, ya bayyana yadda shi da iyalin sa suka tsallake rijiya da baya, bayan fashewar wani abu da ya haddasa rugugi mai ƙarar gaske a Ibadan.
Iyiola ya ce rugugin wanda kusan yawancin unguwanni da dama an ji tashin ƙarar, ya lalata masa gida, saboda a kan layin da shi da iyalan sa ne rugugin ya tashi.
Iyiola ya ce gidan sa ya lalace, har sai da abokin sa ya ba shi wurin da zai kwana shi da iyalin sa.
Ya kuma ce ya yi asara ta miliyoyin nairori sanadiyyar tashin rugugin.
“Ni ma ina ɗaya daga cikin mazauna layin Dejo Oyelese. Gida na ya samu lahani sanadiyyar fashewar rugugin da ya faru a ranar Talata. Mu na cikin kallon ƙwallo kawai sai muka ji rugugin ƙarar fashewar wani abu.
“Dukkan ƙofofin gida na waɗanda ke kulle sai da ƙarfin jijjigar rugugin ya buɗe su da ƙarfin tsiya. Haka tagogi da rufin ɗakuna duka. Lamarin fa ya yi muni sosai.
Tashin ƙarar dai ta halaka mutum 2 kuma ta jikkata mutum 77.
“Binciken farko da aka gudanar ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun gano wasu masu haƙar ma’adinai ba da lasisi ba ne ke zaune a ɗaya daga cikin gidajen da ke kan layin. Su ne ke ajiye da nakiyoyin da suka fashe.”
Yayin da ake ci gaba da bincike, an bayyana cewa an gano waɗanda suka ajiye nakiyar, kuma za a gurfanar da su a hukunta su.
Gwamna Seyi Makinde da ya ziyarci wurin, ya bayar da umarnin a yi wa waɗanda suka ji rauni magani da kulawa kyauta, shi zai biya kuɗaɗen maganin da na kula da jiyyar su.
Kuma zai bayar da wurin zama na wucin gadi ga waɗanda gidajen su suka lalace sanadiyyar fashewar nakiyar.
Gidaje da dama da ke kusa da nesa tsawon kilomita da dama daga inda abin ya faru, duk sun lalace.
Discussion about this post