Bayan ruguza hukumomin gudanarwar Bankin Union, Polaris da Keystone a ranar Laraba, tare da sauke shugabannin bankunan, Babban Bankin Najeriya, CBN ya naɗa wa bankunan sabbin shugabanni.
Cikin wata sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na CBN, Makama Sidi Alli ya fitar, an naɗa Yetunde Oni matsayin Shugaba kuma Manajan Daraktan Union Bank, shi kuma Mannir Ubale Ringim Babban Darakta.
Shi kuma Bankin Keystone an naɗa masa Hassan Imam Shugaba kuma Manajan Darakta, yayin da Chioma A. Mang aka naɗa ta Babbar Darakta.
Bankin Polaris an naɗa masa Lawal Mudassir Omokayode Akintola Manajan Darakta, sai Onyeka Ofikulu Babbar Darakta.
CBN ya ce naɗin na su ya fara aiki nan take.
Sai dai CBN Bai bayar da tarihin waɗanda aka naɗa ɗin ba. Amma binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar ya nuna cewa Yetunde Oni da aka naɗa shugabancin Union Bank, an ɗauko ta ne daga shugabancin Standard Chartered Bank na Saliyo.
Shi kuma Hassan Imam na Keystone Babban Darakta ne a Fedility Bank.
Mudassir Lawal kuma da aka naɗa Bankin Polaris, Babban Darakta ne a Sterling Bank.
CBN ta rushe shugabannin Union Bank, Polaris da Keystone saboda ƙin bin dokar Tsarin Hada-hadar Kuɗaɗe Sashe na 12(c), (f), (g), (h) na Doka ta 2020.
Sauran dalilan ƙwace bankunan sun haɗa da shiga harƙallar da ke kawo barazana ga tsarin hada-hadar kuɗaɗe.
Discussion about this post