Ana zargin kwamishinan matasa da wasanni na jihar Taraba Joseph Joshua da samun digiri na bogi daga wata jami’a a jamhuriyar Benin.
Wannan zargi na kunshe ne a cikin wata wasikar koke da aka rubuta zuwa ga hukumar tsaro ta farin hula (SSS) da rundunar ‘yan sandan jihar.
Wani lauya a Jalingo Nasiru Muhammed ne ya rubuta wasikar da ke dauke da kwanan wata 15 ga Janairu a madadin wani Sulaiman Adamu.
“Adamu ya bayyana mana cewa a lokacin da majalisar dokokin Taraba ta tattance Joseph Joshua a matsayin kwamishinan matasa da wasanni ya gabatar da digiri BSc a kwas din information Technology ESGT daga wata jami’a a Cotonou dake Jamhuriyar Benin
“Da wannan digirin ne Majalisar dokokin ta tattance shi da har ya zama kwamishinan matasa da wasanni.
“Sannan ko da ake tattance shi Joseph Joshua bai gabatar da satifiket din kammala yi wa kasa hidima ba na NYSC ko shaidar rashin yin NYSC ɗin.
Bisa ga haka ne muke kira da gudanar da bincike kan digiri din da Joseph ya gabatar.
“Adamu ya kuma fada mana cewa bisa ga binciken da ya gudanar babu lokacin da Joseph ya bar kasar nan zuwa Jamhuriyar Benin domin karatu.
“Muna sa ran cewa ofishin ku mai daraja zai binciki Joseph Joshua da nufin gano adadin lokutan da ya ziyarci jamhuriyar Benin domin yin karatu, shekarun da ya yi da fasfo dinsa da ya yi tafiya da shi domin tabbatar da ya ziyarci kasar a lokacin da ya yi iƙirarin ya samu satifiket din.
Wakilin PREMIUM TIMES ya kira Joseph a wayar hannu inda yake cewa bashi da nacewa illa a jira sakamakon bincike daga jami’an tsaro.
Da yake tattaunawan da wakilin jaridar jami’in hulda da jama’a na rundunar Usman Abdullahi ya ce bashi da masaniya kan wasikar.
“Har yanzu ban ga kwafin takardar koken ba.
Idan ba a manta ba ministan ilimin Tahir Mamman ya kafa kwamitin domin gudanar da bincike kan jami’o’in kasashen wajen dake bai wa ‘yan Najeriya satifiket din boge.
Discussion about this post