Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta kama wata matar aure mai suna Hafsat Surajo mai shekaru 24 da haihuwa bisa zarginta da daba wa hadiminta mai suna Nafi’u Hafiz wuka har lahira.
Rundunar ‘yan sandan ta ce lamarin ya faru ne a Unguwa Uku da ke karamar hukumar Taurani a jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Hussaini Gumel ne ya tabbatar da hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Juma’a.
Ya ce a ranar 21 ga watan Disamba da misalin karfe 0700 ne aka samu rahoto daga wani Hafizu Salisu na karamar hukumar Bauchi, cewa an kira shi a waya daga wani Daiyanu Abdullahi na Unguwa Uku Kano, cewa dan uwansa Nafi’u Hafiz ya rasu.
Ya bayyana cewa, a lokacin da dan’uwan ya isa gidan a Unguwa Uku, sun ga raunuka da dama a sassa daban-daban na jikin mamacin da ake zargi wuka ne.
Kwamishinan ‘yan sadan ya ce an fara bincike akai kuma nan bada dadewa ba za a bayyana sakamakon binciken.
Gumel ya bayyana cewa wanda ake zargi ta amsa laifin aikata laifin ita kadai ta hanyar daba wa marigayin wuka a sassa da dama na jikinsa.
“An kama mijin ta mai suna Dayyabu Abdullahi da maigadin gidan Malam Adamu da laifin kokarin hada baki da matar a rufe maganar ta hanyar neman boye abinda ya faru.
Discussion about this post