Wani wawakeken rami wanda girmansa zai iya dauke duniyarmu da muke ciki guda 60 ya bude a kan duniyar rana, kamar yadda masana kimiyya suka ce.
BBC HAUSA ta buga cewa ramin, wanda aka hango yankin da ya bude ya yi duhu, wanda a turance ake kira coronal hole, ya bude ne a kan doron kwallon ranar.
An tsinkayi wannan rami ne daga wata cibiyar lura da sararin samaniya ta Hukumar bincike kan sararin samaniya ta Amurka (NASA), tsakanin ranakun 2 da 4 ga wannan wata na Disamba.
Irin wadannan ramuka da kan faru a kan doron rana ba kamar ramuka ne irin na duniyarmu ba, sai dai wani yanki ne na jikin duniyar ranar da kan zamo ba ya da tsananin zafi kamar sauran bangarorinta.
Irin wadannan yankuna kan zamo sun yi duhu idan aka hango su ta na’urar dauko hoton duniyoyi, inda za a ga cewa sauran bangarori na rana wadanda ke da cikakken zafi su kuma sun yi haske kuma sun fi cunkushewa.
Discussion about this post