Wani farfesan kiwon lafiyar dabobbi dake aiki da Jami’ar fasaha ta Akure (FUTA), Bamidele Osho ya bayyana cewa wasu sinadaran hada farfesu da ake da su a Najeriya na dauke da abubuwan inganta lafiyar mutum da dabobbi.
Farfesan ya fadi haka ne a jawabin da ya yi mai taken ‘Amfani da dabarun gargajiya domin inganta lafiyar dabobbi’ a makon jiya.
Oshi ya lissafo wasu kayan hada farfesu da ake da su a kasar nan kamar su citta, tafarnuwa inda yake cewa wadannan kayan hadin farfesun na dauke da sinadarin warkar da cututtuka a jikin dabba da mutum sannan suna iya kare mutum ko dabba daga kamuwa da cututtuka.
Ya kuma ce sinadarin na da ingancin hana abinci saurin lalacewa.
“Ana iya amfani da sinadarin dake cikin kayan hada farfesu wajen samar da maganin guba, kare mutum daga kamuwa da ciwon gyambon ciki wato ‘Ulcer’ da kare yara daga kamuwa da cutar ‘Rickets’ wato cutar dake kama kasusuwan yara a dalilin rashin samun sinadarin ‘Vitamin D’.
Bayan haka farfesan ya bayyana amfanin da dabarun gargajiya ke da su wajen kula da dabbobi inda yake cewa hada dabarun gargajiya da na bature dabara ce da zai taimaka wajen gano hanyoyin da suka fi dacewa wajen kula da lafiyar dabbobi.
Osho ya kuma yi kira ga gwamnati da ta ware kudaden da za a yi amfani da su wajen gudanar da bincike kan amfanin dabarun gargajiya domin inganta lafiyar dabbobi da na mutane.
Discussion about this post