Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong, ya ce har yanzu bai yanke shawara kan ko ya dare kujerar sa a majalisar dattawa ba ko kuma ya ci gaba da zama minista.
Ya ce har yanzu a rude yake ya kasa yanke shawara.
A watan Nuwamba ne kotun daukaka kara da ke Abuja ta kori Napoleon Bali na jam’iyyar PDP a matsayin dan majalisar dattawa mai wakiltar Filato ta Kudu bisa rashin tantance shi da kyau a matsayin dan takarar jam’iyyar a zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Faburairu.
Daga nan ne hukumar zabe INEC ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ga Lalong a Abuja, lamarin da ke nuna cewa akwai yiwuwar ministan ya ajiye mukaminsa na minista ya zama dan majalisar tarayya.
Ni yanzu addu’ar ku na ke bukata Allah ya yi min zabi, ko sanata ko minista, yanzu na rasa wanne zan yi.
Discussion about this post