Ciwon daji, wanda aka fi sani da kansa, ya yi ajalin Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.
Akeredolu, wanda ya shafe watanni da dama ya na jiyya a asibitin Jamus, ya rasu ranar Talata, ƙarfe 2 na dare, wayewar garin Laraba.
Wani babban jami’in gwamnatin Jihar Ondo, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES da labarin rasuwar gwamnan.
Akeredolu ya daɗe ya na jiyyar da ta kai shi ga kasa zama ya gudanar da mulki tsawon dogon lokaci.
Discussion about this post