Gwamnatin Jihar Kano ta kori ma’aikata 3,234, waɗanda ta ce ba su cancanci shiga aikin gwamnatin jihar ba.
Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Abdullahi Bichi, ya ce an sallame su ne bayan an kammala aikin tantance ɗaukar ma’aikatan da Gwamnatin Abba Kabir-Yusuf ta yi.
Tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya shafe shekaru bai ɗauki ma’aikata a lokacin mulkin sa ba, sai da ya bari wa’adin sa ya zo ƙarshe ya yi ta rubdugun ɗaukar ma’aikata, lamarin da aka riƙa kukan cewa ya yi haka ne don ya haɗa su faɗa da gwamnan da zai gaje shi.
Cikin watan Yuni Abba ya dakatar da ɗaukar ma’aikata sama da 10,000 waɗanda Ganduje ya yi lokacin da ya zo sauka.
Abba ya ce an ɗauke su ba bisa ka’ida ba, sannan kuma akasarin su ba su ma cancanci a ɗauke su aikin ba, ko da kuwa aikwai guraben su ɗin.
A taron manema labarai, Bichi ya ce bayan an tantance ma’aikatan, wasun su an gano cewa ƙananan yara ne, wasu kuma satifiket ɗin karatun su na bogi ne, amma kuma duk an saƙa sunayen su a jerin masu karɓar albashi.
“An gano cewa 9,332 daga cikin su sun cancanci ɗauka aiki, daga cikin 12,556 ɗin da aka tantance.
“Ya ce lokacin da waccan gwamnatin ta ɗauke su aiki, ba a tantance su ba, ta hanyar da ta dace.
Ya ƙara da cewa da yawa daga cikin su ma ɗaliban sakandare ne, har ma da na ƙaramar sakandare, wasu kuma su na shekarar farkon shiga jami’a.
Discussion about this post