Wani magidanci mai shekara 43 Muhammadu Ali ya gamu da ajalinsa yayin da ya je gwajin lakanin bindiga a jihar Bauchi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ahmed Wakil ya sanar da haka wa manema labarai ranar Talata.
Wakil ya ce Ali mazaunin kauyen Damaiwa dake karamar hukumar Zaki ne inda wata rana ya bi wani boka mai suna Danladi Ya’u da wasu mutane uku cikin dajin dake kauyen sannan bayan ya daura layar da bokan ya bashi sai shi bokan ya dankara masa harsashin bindiga.
Ya ce nan take Ali ya yanke jiki ya fadi mutacce.
“Rundunar ta samu labarin abin da ya faru ranar 31 ga Oktoba da karfe 8:30 inda cikin gaggawa jami’ai suka shiga dajin suka garzaya da Ali asibiti amma likita ya sanar cewa ai Ali ya riga mu gidan gaskiya.
Wakil ya ce ‘yan sanda sun kama Ya’u da wani mutum daya amma sauran mutanen sun gudu.
Ya ce rundunar za ta ci gaba da farautar mutanen da suka gudu tare da gudanar da bincike akan ainihin abinda ya faru.
Discussion about this post