Sojojin l Najeriya dake aiki a karkashin rundunar ‘Operation UDO KA II’ sun ragargaza maɓoyar mahara ‘yan kungiyar IPOB hudu a jihar Imo ranar Lahadi.
Sojojin sun kashe ‘yan kungiyar biyu sun kama mutum hudu.
Shugaban rundunar ‘Operation UDO KA II’ Jonah Unuakhalu ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar ranar Litinin a garin Enugu.
Unuakhalu ya ce maɓoyar maharan da suka far wa suna kauyukan Ihube, Aku da Umulolo a karamar humar Okigwe.
Ya ce dakarun sun ci karo da bamabamai da maharan suka dasa yayin da suke hanyar zuwa mabuyar.
Da yawa daga cikin ƴan IPOB da sojojin suka yi batakashi da sun gudu da raunin harsashi a jikinsu.
“Maharan kan yi amfani da dazukan domin yin aiyukkan asiri da suka hada da cin naman mutum, kisa da dai sauran su domin tsorata mutane.
“Jami’an tsaron sun rusa bukkokinsu da wani da ke kamada ɗakin tsafe tsafen su
da a ke kira Amobi Chinoso Okafor wanda aka fi sani da Temple.
Unuakhalu ya ce sojoji sun kama kudaden Biafra, babur ɗin tsere daya da wasu hudu da na’urar Sola.
Sauran abubuwan da suka kama sun hada da siminti da tankin man fetur Wanda dakarun ke zargin maharan sun kwace daga hannun mai shi.
Discussion about this post