Jami’ar Tehran, ta bai wa shehin malami Ibrahim El-Zakzaky lambar yabo ta digirin girmamawa (Honoris Causa) kan Ilimin Duniya: Zaman Lafiya. da Magance Rikice-Rikice.
A cewar wata sanarwa da Fatima Hassan ‘yar kungiyar IMN ta fitar, taron ya gudana ne a wani taro da jami’ar ta shirya a ranar Asabar.
Dakta Hassan ta ruwaito jami’ar na cewa an bayar da wannan karramawar ne sakamakon amincewar da majalisar dattawan ta ta yi.
An ga hotunan El-Zakzaki tare da iyalan sa a ƙasar Iran, tare da shugaban addini na kasar a makon jiya.
Discussion about this post