Kotun Westminster da ke birnin Landan ta bayar da belin tsohuwar Ministar Fetur ta zamanin mulkin Goodluck Jonathan, Diezani Alison-Madueke, bayan ta bayyana a kotun yau ranar Litinin.
An bada belin ta kan kuɗi fam na Ingila 70,000, sannan aka bari ta koma gida.
Sannan kuma an kafa mata sharuɗɗa da ƙa’idojin walwala, inda kotun ta hana ta fita daga cikin gidan ta, tun daga ƙarfe 11 na dare har zuwa ƙarfe 6 na safe.
Bayan wannan, kotun kuma ta umarce ta ta maƙala na’urar gane duk inda ta shiga a lokacin da ta fita daga gida da rana.
PREMIUM TIMES ta buga labarin bayyanar Diezani a kotu yau Litinin.
A ranar 30 ga Oktoba ma Diezani za ta gurfana a wata kotun, bisa wasu tuhume-tuhumen rashawa, harƙalla da daƙa-daƙa.
Discussion about this post