Najeriya ta cika shekaru 63 bayan samun ‘yanci, a wani lokacin da ‘yan ƙasar ke cikin jimamin raɗaɗin tsadar rayuwa da fuskantar gagarumin tashe-tashen hankulan kashe-kashen da ba a san rana ko lokacin kawo ƙarshen su ba.
A can shekarun baya da ƙasar ke kwance lafiya, da har yau a irin wannan lokacin ana nan ana ta shagulgula da rafsar ganguna, saboda buki ne na murna da nishaɗi.
Maganar gaskiya kuma mai ɗaci dai a yanzu ita ce taurarin da ke haskaka Najeriya a da can, yanzu kuwa babu su, sun disashe, ko kuma duhu ya cim masu.
Ita kan ta Gwamnatin Tarayya ta san da haka, domin a makon da ya gabata Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume da kan sa a lokacin da zai yi sanarwar zagayowar ranar samun ‘yanci, cewa ya yi, “ba za a yi shagulgula ba, saboda matsanancin halin ƙuncin rayuwa da matsin tattalin arzikin da ake ciki.”
Lokacin ya zo daidai da lokacin da NLC TUC suka yi yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyu. Kuma a ranar Talata ce za su tsunduma yajin aikin duk ƙasa baki ɗaya.
Za a tafi yajin aikin, saboda Gwamnatin Tarayya ta ƙasa magance wa talakawa raɗaɗin tsadar rayuwar da ke kwankwatsar su, watanni huɗu kenan da ta yi alƙawarin aiwatarwa, tun bayan cire tallafin fetur da Shugaba Tinubu ya yi, a ranar da aka rantsar da shi.
Idan gwamnati ta yi sakaci ta bari aka tafi yajin aiki, to tattalin arzikin da ke tangal-tangal zai ƙara takwarkwashewa.
Wannan dai ba ita ce Najeriyar da iyayen mu waɗanda suka yi fafutikar kafawa suka bar mana.
A ranar Talata sai da lalacewar darajar Naira yi yi munin da ta kai ana sayen dala 1 a Naira 1,054 a kasuwar ‘yan canji.
Babbar Tashar Rarraba Hasken Lantarki ta Ƙasa ta durƙushe sau uku cikin wata ɗaya, yayin da adadin wutar da ake samu ɗin ma ba ta wuce migawat 4,100 ba Najeriya, mai yawan al’umma sama da miliyan 200. Amma Afrika ta Kudu mai yawan al’umma miliyan 59.3 na samun hasken lantarki har migawat 58,095.
Daga cikin manyan matsalolin da su ka haifar mana waɗannan abubuwan kaico, akwai yadda karta-kartan ɓarayin gwamnati ke wasoson dukiyar al’umma, mummunan cin hanci da rashawa, rashin tsarin iya gudanar da mulki, rashin hukunta waɗanda suka kwashi dukiyar jama’a da yadda mutane nagari suka yi ƙaranci matuƙa a kan shugabancin jama’a.
Babu babban abin takaici kamar a ce ƙasa irin Najeriya mai arzikin man fetur, kuma mafi ƙarfi a Afrika, amma a ce ba ta iya tace ɗanyen mai a cikin ƙasa.
Dalili kenan hakan ke jawo satar kuɗaɗe muraran da sauran hanyoyin asarƙala da harƙalla iri daban-daban. Cikin 2020 Najeriya ta sayo fetur na dala biliyan 1.32. Wannan kaɗan ma kenan.
Wani abin tayar da hankalin mai hankali shi ne bayanin da Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya yi, inda ya ce Gwamnatin Muhammadu Buhari ta kashe dala biliyan 19 wajen gyaran matattun matatun mai na ƙasar nan, amma ba a samu biyan bukata ba tsawon shekaru takwas.
Sannan kuma shiru ka ke ji ba a wani hoɓɓasa domin ƙwato waɗannan maƙudan kuɗaɗe daga hannun ‘yan kwangila.
Matsaloli ko da ina sun kamo hanyar durƙusar da Najeriya. A Arewa maso Gabas ana fama da Boko Haram tsawon shekaru 13 kenan. Arewa maso Gabas na fama ‘yan bindiga. Masu garkuwa da mutane sai ɓarna su ke yi a faɗin ƙasar nan, masu neman ɓallewa daga Najeriya sun hana kan su da ‘yan yankin su zaman lafiya a Kudu maso Gabas. Su ma Kudu maso Kudu masu arzikin man fetur na fama da tasu matsalar, wadda saboda arzikin ɗanyen mai a yankin ta zama matsalar da ta shafi ƙasa baki ɗaya.
Yawan mutanen da su ka rasa rayukan su kama daga fararen hula da jami’an tsaro ba su ƙirguwa, sai dai ƙiyastawa, kintace ko shaci-faɗi. Kai ko da yaƙi ne muraran aka gwabza, ɓarnar ba za ta kai munin ta yanzu ba.
A 2021 Hukumar UNDP ta ce kashe-kashen Boko Haram a Arewa maso Gabas ya ci rayuka 350,000, mafi yara ‘yan shekaru biyar abin da ya yi ƙasa.
Wannan ƙazamin ta’addanci ya ci aƙalla Dala biliyan 100, kamar yadda UNICEF ta bayyana.
A gefe ɗaya kuma akwai yara miliyan 20 masu gararamba a gari, waɗanda ba su zuwa makaranta. Duk duniya kuwa Najeriya ce mai yawan irin waɗannan ƙananan yara haka.
Ga kuma nagartar ilmin shi kan sa a Najeriya ya taɓarɓare. Matasa sai tururuwa suke yi zuwa Turai da Amurka. Lalacewar ta yi yawa wasu na nausawa Togo da Ghana da Afrika ta Kudu don neman ilimi.
Tsakanin 2017 zuwa 2022, ‘yan Najeriya 99,985 suka shiga jami’o’i daban-daban a Birtaniya. Haka dai ƙididdigar HESA ta tabbatar.
A Arewacin Najeriya kuwa, wata guguwa ake fama ita, wadda ke ɗaukar dandazo-dandazo na matasa su na tafiya Aljeriya da Libiya domin yin aikin ƙarfi da sauran ‘yan sana’o’in hannu. Da dama kuma sun koma cikin manyan garuruwan Nijar su na sana’o’in gini, gyaran wuta, ado da kwalliyar sabbin gidaje da sabbin ɗakuna ko ayyukan kafinta.
Babu ƙasar da za ta iya bunƙasa matsawar ana satar biliyoyin daloli kamar irin yadda masu mulki da manyan ma’aikata ke ɗibga sata a Najeriya. Shi ya sa duk da ɗimbin arzikin albarkatun ƙasa da ake da shi a ƙasar nan, akwai mutum miliyan 133 da aka haƙƙaƙe su na fama da matsanancin talauci, fatara da kuma rayuwa a cikin ƙunci.
Shirme da raina darajar ɗan Adam ne a ce wai gwamnati na raba wa mutum 12 buhun shinkafa ɗaya, da sunan rage masu raɗaɗin tsadar rayuwa. Ya kamata Tinubu ya tashi tsaye ya lalubo wasu hanyoyin fitar da ‘yan Najeriya daga ƙuncin da aka jefa su. Amma raba mudun shinkafa da ledar taliya a matsayin rage raɗaɗin tsadar rayuwa, tamkar yaudara ce.
Discussion about this post