Isra’ila ta umarci duka Falasɗinawa mazauna Arewacin Gaza su yi kaura su koma yankin kudancin Gaza cikin sa’o’i 24 ko kuma duk ta dagargaza su.
Isra’ila ta ce za ta dagargaza yankin Arewacin Gaza kaf din ta domin gamawa da ‘yan kungiyar Hamas.
Jiragen yakin Isra’ila na cigaba da yi wa yankin Gaza luguden bamabamai babu kakkautawa. Yara, mata, da masu ciki na daga cikin wadanda ke rasa rayukan su a harin da Isra’ila ke cigaba da kai wa Falasɗinawa.
Kasashen duniya na cigaba da yin tir da nuna kyamar su ga abinda Isra’ila ke yi yankin Gaza.
Akalla Falasɗinawa 70 ne suka mutu yayin da suke yin kaura zuwa Kudancin.
Bam ya kashe dan jarida, wasu uku sun jikkata
Ɗan jarida daya ya rasa ransa, yayin da wasu hudu suka jikkata a hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai kusa da garin Alma asShaab da ke kan iyakar kasar Lebanon a ranar Juma’a.
An kashe Essam Abdullah na kamfanin dillancin labarai na Reuters, yayin da wakilan AFP da Aljazeera suma suka jikkata a harin da Isra’ila ta kai.
An kai ‘yan jaridar da suka jikkata zuwa wani asibiti da ke kusa da su, ko da yake har yanzu ba a san girman raunin da suka samu ba.
Wani dan jarida ya bayyana wa Aljazeera cewa, ‘ Dagangar Isra’ila ta kai wa motar ‘yan jaridar hari, domin sun saka tambarin ‘yan jarida sun kuma saka kayan su sannan dauke da kamarorin su da kayan aiki.
Discussion about this post