Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, ta bayyana cewa mijin ta ba da aljanu ya ke aiki ba, amma dai ya na aiki sosai domin gyara Najeriya ya maida ta bisa saiti sosai.
Remi ta bayyana haka a ranar Lahadi, a Abuja, lokacin da ta halarci taron addu’o’in cikar Najeriya shekaru 63 da samun ‘yanci.
Ta ce gwamnatin Tinubu ta gaji matsalolin da ake fama da su ne a yanzu, amma kuma ya na bakin ƙoƙarin sa wajen ganin ya magance matsalolin, ba tare da ya na ɗora laifin a kan kowace gwamnatin da ta shuɗe ba.
“Ba mu gaji komai ba sai matsalolin da suka taru suka cakuɗe tsawon shekarun baya. Ba mu hau mulki don mu ɗora laifin a kan gwamnatocin baya ba, amma mun hau mulki ne don mu gyara ɓarnar da aka rigaya aka yi.
“Miji na fa ba da aljanu ko rauhanai ya ke aiki ba. Amma zai gyara matsalolin da ke damun ƙasar nan. Kuma na yi amanna za mu samu zaman lafiya a ƙasar nan.” Inji Remi Tinubu.
PREMIUM TIMES Hausa ta ruwaito jawabin Shugaba Tinubu, wanda shi ma ya bayyana cewa, bai so Najeriya ta afka cikin raɗaɗin ƙuncin da ake fama da shi ba.
A rahoton, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa a matsayin sa na Shugaban Ƙasa, ba ya farin ciki da jin daɗin jagorantar al’ummar da ke fama da mawuyacin halin da ake fuskanta yanzu a ƙasar nan.
A jawabin sa a yau Lahadi domin tunawa da zagayowar ranar samun ‘yancin ƙasa, shekaru 63 da suka gabata, Tinubu ya ce, “ina ma a ce ba a shiga cikin mawuyacin halin da ake fuskanta yanzu a ƙasar nan ba.”
A jawabin na sa, ya ce tsare-tsaren tattalin arzikin ƙasa da gwamnatin sa ta bijiro da su masu kaifi da zafi da ƙunci ne. To amma fa wannan kaɗai ce hanyar da za a iya bi nan gaba kaɗan a cimma sauƙi da walwala da yalwar arziki.
Ya ce ‘yan Najeriya nagartattun mutane ne, “dukkan mu daidai da juna m ke, babu wani da ya fi wani a cikin mu. Nasarar da Najeriya ta samu ce za ta iya tantance mu.”
Tinubu ya ce raɗaɗin ƙunci da tsadar rayuwa da ake ciki a yanzu ba mai ɗorewa ba ne dimun-da’imun. Ya ce “nan gaba kaɗan wannan wahala za ta zama tarihi.”
Da ya koma kan alƙawurran da ya yi a farkon mulkin sa, Tinubu wanda a yau ya cika watanni huɗu kan mulki, ya ce ya yi alƙawarin sauya fasalin tattalin arzikin Najeriya, tare da zamanantar da shi. Kuma ya yi alƙawarin kare rayukan ‘yan Najeriya da su da dukiyoyin su.
“Na ɗauki gaban-gabarar cire tallafin fetur ba don ƙaƙaba wa ‘yan Najeriya wahala ba, sai don samar masu rayuwa mai sauƙi da yalwar arziki nan gaba ba da daɗewa ba.
“Saboda haka ina gani da ido na, kuma ina ji da kunne na irin mawuyacin halin da ake ciki. Roƙo na shi ne a ƙara juriya, za a fita daga wannan ƙunci a shiga cikin walwala.” Inji Tinubu.
Discussion about this post