Jam”iyyar APC ta yi kira ga Ministan Harkokin Shari’a Lateef Fagbemi ya sa a binciki Atiku Abubakar da Peter Obi, bisa kalaman su na zargin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da yin fojare na takardun karatun jami’a da na shiga jami’a.
Jam’iyyar ta ce Antoni Janar ya binciki Atiku, ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP da Peter Obi ɗan takarar shugaban ƙasa na LP a zaɓen Fabrairu, 2023.
Sakataren APC na Ƙasa, Ajibola Bashiru ne ya bayyana haka a lokacin da aka yi wata tattaunawa da shi a gidan talabijin na Channels, a ranar Laraba.
Bashiru wanda tsohon lauya ne kuma tsohon malamin jami’a, ya ce kalaman da Atiku da Tinubu suka firzas daga cikin bakunan su, furuci ne na cin amanar ƙasa, idan aka yi nazarin su.
Ya ce a bincike su saboda sun yi kalamai na cin amanar ƙasar nan a lokacin da su ke maganganu dangane da takardun kammala digirin Tinubu.
Ya yi kiran sa’o’i kaɗan bayan Peter Obi ya ƙalubalanci Bola Tinubu cewa ya fito ya bayyana wa ‘yan Najeriya haƙiƙanin asalin sa da ko shi wane ne.
Ministan Shari’a kuma Antoni Janar, Tinubu ne ya naɗa shi Minista kwanan baya, sannan kuma kafin naɗin sa, shi ne shugaban gungun lauyoyin da ke kare Tinubu a kwatagwangwamar shari’ar zaɓen da ake tafkawa tsakanin shugaban ƙasar da Atiku da kuma Peter Obi.
A ranar Litinin ce idan ba a manta ba, Atiku ya ce hadiman Tinubu na ruɗar da jama’a, su na kange su daga gane gaskiya.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, kuma ɗan takarar shugabancin ƙasa a zaɓen 2023, Atiku Abubakar na PDP, ya yi zargin cewa hadimai da ‘yan jagaliyar Tinubu na kange jama’a daga fahimtar irin bogin da takardun shaidar karatun Jami’ar Chicago na shi Shugaba Tinubu ɗin.
Ya ce tsawon mako ɗaya ke nan tun bayan damƙa kwafen takardun da aka yi, an yi ta ƙoƙarin ganin ana ta sauya yadda gaskiyar lamarin ya ke.
Atiku ya ce hadimai da ‘yan jagaliyar Tinubu sun yi ta karkatar da mutane, tare da ruɗar da su daga fahimtar ainihin irin abin kunya da bahallatsar da Tinubu ya tafka, ta hanyar shirya takardun bogi.
Haka Atiku ya bayyana a cikin wata sanarwar da Kakakin sa Paul Ibe ya fitar a ranar Lahadi.
Tuni dai Atiku ya ɗaukaka ƙara, tun ma kafin ya karɓo kwafen takardun karatun Tinubu daga Jami’ar Jihar Chicago, wanda ya bayyana a ranar Talata.
Lauyan Tinubu mai suna Oluwole Afolabi, ya bayyana wa PREMIUM TIMES a wata tattaunawa da shi cewa, “Takardun Tinubu ba su da wata matsala. Amma duk wanda ke fa wata tantama, sai ya kawo hujja.” Inji Lauyan Tinubu.
Sai dai Atiku ya ce, “wasu hadimai da ‘yan jagaliyar Tinubu su na ta ƙoƙarin karkatar da mutane daga fahimtar yadda gaskiyar maganar ta ke. Yayin da wasu kafafen yaɗa labarai kuma musamman wata guda ɗaya, ta na ta ƙoƙarin fassara lamarin a baibai.
“To maganar gaskiya dai ita ce, Shugaba Bola Tinubu ya damƙa wa INEC satifiket na bogi. Sannan kuma ya yi rantsuwa a kan na gaskiya ne.”
Daga nan sai Atiku ya ce “idan har Tinubu ba zai kunyar duniya ya yi murabus ba, domin kare ɗan sauran mutuncin sa, to hadiman sa da ‘yan jagaliyar sa su daina kantara wa ‘yan Najeriya da duniya ƙarairayi.”
Discussion about this post