Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta bayyana cewa akwai yiwuwar akalla mutum 15,060 sun kamu Diphteria a kasar nan.
Zuwa yanzu an samu tabbacin mutum 9,478 da suka kamu da cutar daga kananan hukumomi 137 dake jihohi 20 da Abuja.
Shugaban hukumar Ifedayo Adetifa wanda ya sanar da haka a taron manema labarai ranar Alhamis ya ce da dama daga cikin wadanda suka kamu da cutar ‘yan shekara 1 ne zuwa masu shekaru 14 sannan jarirai na da kason kasa da kashi daya na yawan wadanda suka kamu da cutar.
Har yanzu dai jihar Kano ce jihar da ta fi fama da yaduwar cutar inda a jihar mutum 7,747 suka kamu sai kuma jihar Yobe dake bi mata da mutum 841.
Yaduwar cutar Diphtheria a Najeriya
Hukumar ta ce jihohin dake fama da yaduwar cutar sun hada da Bauchi – 369, Katsina – 275, Borno -164, Jigawa-24, Kaduna-18, Legas-8, Zamfara- 7, FCT- 7, Gombe- 5, Sokoto– 4, Osun- 3, Niger-2.
Jihohin Cross River, Enugu, Imo, Nasarawa, Kebbi da Taraba duk sun samu mutum daya da ya kamu da cutar.
Rigakafin cutar
Shugaban hukumar NPHCDA Faisal Shuaib ya ce gwamnati ta yi wa yara 1,692,762 ‘yan watanni shida zuwa shekara hudu allurar rigakafin cutar da maganin ‘Pentavalent vaccine’.
Ya kuma ce gwamnati ta yi wa yara 3,166,419 masu shekaru 4 zuwa 14 rigakafin cutar da maganin Td.
Ya ce an fara yi wa yara allurar rigakafin ranar 23 ga Satumba a kananan hukumomi 56 dake jihohi 7 a kasar nan.
Ya ce yanzu burin hukumar shine yi wa yara 1,111,310 allurar rigakafin cutar da maganin Td sannan da yara 544,737 da maganin ‘Pentavalent vaccines’ a zango na biyu.
Shuaib ya ce jihar Katsina ta yi wa yara 403,252 allurar rigakafin cutar da maganin Td sannan da yara 255,075 da maganin ‘Pentavalent vaccines’.
Sannan jihohin Kaduna, Bauchi, Borno, Jigawa da Yobe sun zage damtse wajen yi wa yara allurar rigakafin cutar a jihohinsu.
Discussion about this post