Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta bayyana cewa dakarun ta sun kama dalibai hudu ‘yan kungiyar asiri ‘Black Axe’.
Jami’an tsaron sun kama daliban yayin da suke taron marabtan wasu sabbin mambobin kungiyar da suke yi a bayan gari kusa da Jami’ar Abubakar Tafawa-Balewa dake Gubi kusa da hanyar Kano zuwa Bauchi ranar 2 ga Satumba.
Kakakin rundunar Ahmed Wakil ya sanar da haka a wata takarda da manema labarai suka samu ranar Juma’a.
Wakil ya ce dakarun sun kama Eric Nuhu mai shekara 23 Kuma dan aji 500L dalibin jami’ar ATBU, Zaharaddeen Hassan mai shekara 19 dalibin kwalejin kimiya da fasaha Bauchi da Daniel Masaka daga karamar hukumar Karu jihar Nasarawa.
“A hannun jami’an tsaro dalibin farko cikin waɗanda aka kama ya ce suna daga cikin sabin mambobin da ake wa wankan shiga ƙungiyar sannan wani abokinsu Abbas Apeh dan aji 500L a jami’ar ATBU sannan sauran tsofaffin ƴan kungiyar ne da suka halarci taron wanke sabbin ƴan kungiyar kungiyar.
Ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike domin kamo sauran ‘yan kungiyar.
Rundunar za ta maka mutanen a kotu domin yanke musu hukunci da zarar sun kammala gudanar da bincike.
Discussion about this post