Shugaban kungiyar likitocin da suka kware a kula da masu fama da cutar dajin dake kama nono na Najeriya ARCON Nwamaka Lasebekon ta bayyana cewa Najeriya ta fi yawan matan da cutar dajin dake kama nono ke kashewa a duniya.
Likitan ta fadi haka ne a taron dakile yaduwar cutar da aka yi a jihar Enugu.
Nwamaka ta ce ya zama dole a dauki matakan dakile yaduwar cutar musamman yadda cutar ke shafan tattalin arziki da Bil Adama.
“ Cutar kan kama mata a lokacin da suke da karfin yin aiki da haihuwa.
Ta ce cutar ya fi kama mata kuma ana iya gadon cutar, rashin cin abincin dake inganta garkuwar jiki na iya haddasa cutar amma kuma shayar da jariri nono na iya samar da kariya ga mace daga kamuwa da cutar.
Nwamaka ya ce kamata ya yi mata su rika yin gwajin cutar lokaci-lokaci amma akwai camfe-camfe da ake yi game da cutar.
“ Mata da dama da suka kamu da cutar sun rika danganta shi da jifa ko sihiri aka yi musu. Maimakon su rika garzayawa asibiti sai wurin Bokaye da malaman tsubbu domin neman magani.
Ta ce kungiyar ARCON ta wayar da kan mutane kan cutar, hanyoyin samun kariya da yadda za a samu maganin cutar.
Nwamaka ta yi kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki da su samar da magungunan cutar a farashi mai sauki domin masu fama da cutar su iya samun magani.
Discussion about this post