Kotun sauraren kararrakin zabe a Jos ta kori sanata mai wakiltar mazabar Filato ta Kudu, Napoleon Bali, da dan majalisar tarayya mai wakiltar Barikin Ladi/Riyom a majalisar wakilai, Peter Gyendeng.
Daga nan ne kotun ta ayyana tsohon gwamnan jihar, Simon Lalong, na jam’iyyar APC a matsayin sahihin zababben sanatan yankin Filato ta Kudu.
Kotun ta kuma ayyana Fom Dalyop na Jam’iyyar Labour (LP) a matsayin sahihin wanda ya yi nasara a zaben mazabar tarayya ta Barikin Ladi/Riyom.
Hukumar zabe, INEC, ta bayyana cewa Lalong da Dalyop sun zo na biyu a zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
‘Yan takarar jam’iyyar APC da LP dai sun bukaci kotun da ta soke zaben Mista Bali (PDP) da Mista Gyendeng (PDP) bisa hujjar cewa PDP ba ta da tsarin jam’iyya mai kyau, don haka ba za ta iya gabatar da ‘yan takarar zaben ba.
‘Yan takarar jam’iyyar APC da LP dai sun bukaci kotun da ta soke zaben Bali (PDP) da Gyendeng (PDP) bisa hujjar cewa PDP ba ta da tsarin jam’iyya mai kyau, don haka ba za ta iya gabatar da ‘yan takarar zaben ba a wancan lokaci.
Sun kara da cewa INEC ba ta bi doka da ka’idojin zabe ba har zuwa lokacin gudanar da zaben.
A hukuncin da kotunan suka yanke Omaka Elekwo (na zaben Sanata) da Muhammad Tukur (na zaben Reps) sun soke zaben ‘yan takarar jam’iyyar biyu saboda kin mutunta umarnin babbar kotun Jos da jam’iyyar ta yi na kin gudanar da zabukan fidda gwani na majalisa kafin zaben gama gari da ya gabata.
Alkalan sun ci gaba da cewa shaidun da ‘yan takarar jam’iyyar APC da LP suka gabatar sun sahihan hujjoji ne inda suka ce duk kuri’un da aka kada na ‘yan takarar PDP lalatattu ne.
Sai dai ana sa ran ‘yan majalisar da aka kora za su daukaka kara kan hukuncin da kotun ta yanke kuma za su ci gaba da rike mukamin har sai an kammala daukaka kara.
Discussion about this post