‘Yan bindiga sun kashe mutum 20 kuma wani mutum daya ya ji rauni a kauyen Kulbe dake karamar hukumar Mangu a jihar Filato.
Wani mazaunin kauyen Jerry Datim ya sanar da haka wa menema labarai ranar Litini a garin Jos.
Datim ya ce maharan sun shigo kauyen da misalin karfe 8:40 na daren Lahadi.
“Maharan sun shigo kauyen suna harbi ta ko ina da hakan ya sa mutane suka fara gudu.
“Maharan sun kashe mutum 20 kuma mutum daya ya ji rauni.
“Mun kira jami’an tsaro sai dai kafin su zo maharan sun arce.
Majiya mai tushe a rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar wa manema labarai cewa rundunar ta fara farautar maharan domin a gama da su.
Discussion about this post