A hadarin jirgin ruwan da aka yi a karamar hukumar Mokwa jihar Neja mutum 26 sun mutu sannan har yanzu ana neman wasu mutum 44.
Hadarin ya auku tsakanin dam din Jabba da Kainji ranar 10 ga Satumba da misalin karfe 8 na safe.
Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta jihar Neja NSEMA ta bayyana cewa akalla mutum 100 ne ke cikin jirgin ruwan a lokacin da hadarin ya auku.
Hukumar ta ce jirgin ruwan ya dauko mutane daga kauyukan Gbajibo, Ekwa da Yankyade zai kai su gonakinsu dake tsallaken ruwan.
Jami’in hulda da jama’a ta hukumar Ibrahim Husseini ya ce hukumar ta hada hannu da karamar hukumar Mokwa domin ganin an gano sauran mutanen da suka bace bayan hadarin.
“Zuwa yanzu mun gano gawar mutum 26, an ceto mutum 30 da ransu sannan muna kokarin gano sauran mutum 44 din da suka rage.
Shugaban karamar hukumar Mokwa Jibrin Muregi ya tabbatar cewa haryanzu ana neman mutanen a raye ko gawarwakin su.
Discussion about this post