Gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya shawarci ƴan takaran shugaban Kasa na PDP da LP, Atiku Abubakar da Peter Obi, su amince da hukuncin kotu, kada su garzaya kotun Ƙoli.
Kotun shari’ar zaɓen shugaban kasa ta yi watsi da kararrakin da jam’iyyun ARM, LP da PDP suka shigar suna ƙalubalantar zaɓen Bola Tinubu na APC shugaban Najeriya.
Dukkan su ƴan takaran basu amince da hukuncin kotun ba, kuma duk sun garzaya kotun koli domin a ci gaba da fafatawa.
Yahaya Bello ya ce da Atiku da Obi za su gane, su hakuri su amince da hukuncin kotun da ya fi musu.
Kamata ya yi su haɗa kan mabiya da magoya bayan su su tausa su, su hakura, amma kotun koli da suka garzaya ba zai haifar musu da ɗa mai ido ba.
Sai dai kuma gwamnan Bello ya umarci sanatocin APC biyu da kotu ta kwace kujerar su, su garzaya kotun Koli.
Discussion about this post