Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta bayyana cewa dakarun ta sun kama shanu 77 da aka sato daga jihar Bauchi.
Rundunar ta ce an kwace wadannan shanu daga wani makiyayi a Bauchi inda daga nan aka kawo su zuwa karamar hukumar Wase dake jihar Filato.
“Dakarun ‘yan sandan dake aiki a Bashar a ranar 19/9/2023 sun samu bayanin cewa ‘yan bindiga sun saci shannun Galadiman Yuli Duguri ranar 11/9/23 daga kauyen Gajin Duguri dake karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi.
“Ƴan sandan tare da hadin gwiwar ‘yan banga da mafarauta sun kama shannu 77 sannan har an maida su hannun Galadiman Yuli Duguri.
Rundunar ta fara farautar ‘yan bindigan da suka aikata haka domin a hukunta su.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Okoro Alawari ya tabbatar cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin mutane a jihar.
Alawari ya yi kira ga mutane da su e ƙa gaggawar kawo karar wani ko wani abin da basu yadda da shi ba ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su.
Discussion about this post